Girka ta kama hanyar amincewa da Paladinu | Labarai | DW | 22.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka ta kama hanyar amincewa da Paladinu

A wani yunkuri na amincewa da Palasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kan ta, 'yan majalisun dokokin kasar Girka sun kada kuri'ar amincewa da Palasdinu.

Hakan ta faru ne tare da halartar Shugaban na Palasdinawa Mahmoud Abas da ke wata ziyara a kasar ta Girka. A cewar Tassos Kourakis da ke matsayin mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar ta Girka, wannan zabe ya kasance wani abu mai babban mahimmanci da zai buda hanya ya zuwa ga amincewa da Falasdinu a matsayin kasa.

Dukannin bangarorin siyasar kasar ta Girka dai da ke majalisar sun kada kuri'ar amincewa da wannan mataki, inda hakan zai bai wa gwamnatin kasar damar daukan dukkan matakan da suka dace kan hakan. Tuni dai Firaminista Alexis Tsipras na Girka ya sanar da kiran sunan Falasdinu a matsayin kasa a dukannin kundayan aikin kasar ta Girka.