Girka ta bude kasuwannin hannayen jari | Labarai | DW | 03.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka ta bude kasuwannin hannayen jari

Ba dai a tsammanin akwai wani hannun jari koda kuwa ɗaya ne da zai samu tagomashi da buɗe kasuwar.

Die Börse in Athen

Kasuwar hannun jari a Girka

Ƙasar Girka ta ɗauki mataki na gaba a batutuwa da sauka shafi tattalin arzikinta inda a ranar Litinin ɗin nan ta buɗe kasuwannin hannayen jarinta a karon farko, tun bayan da aka rufe kasuwannin makwanni biyar da suka gabata. Sai dai a yayin buɗe kasuwar ana tsammanin faduwar darajar hannayen jari.

Masu hada-hada a kasuwannin na hannayen jari a kasar ta Girka da ma wajenta na ganin cewa za a fiskanci faduwar darajar hannayen jarin da zarar an buɗe kasuwar a ranar Litinin din tun da misalin karfe bakwai agogon GMT.

A cewar Takis Zamanis masanin harkokin zuba jari a Girka ya ce ba sa tsammanin akwai wani hannun jari koda kuwa ɗaya ne da zai samu tagomashi a ranar Litinin ɗin nan da za a bude kasuwar.