Girka na zaben raba gardama | Labarai | DW | 05.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka na zaben raba gardama

Firaminista Alexis Tsipras ya shawarci masu zaben da su ce "a'a " ba su goyi baya ba domin zai karfafa matsayarsa idan ya je tattaunawa.

Runfunan zabe sun bude a Girka, na zaben raba gardamar da ya bukaci da su bayyana ra'ayinsu dangane da ko za su amince da tayin tsuke bakin aljihun da masu ba da rancen kasa da kasa suka yi musu. Al'ummar kasar, wadda kowace kasar Turai bashi a yanzu haka, na gab da yanke shawarar ko za ta bijire, ta ki karban tayin tallafin da ya tanadi ta yi tsimi, ta kuma gudanar da wasu sauye-sauye a tsarin kudinta - Wanda Hukumar gudanarwar Turai da babban bankin Turai da Asusun Bada Lamuni na duniya suka yi mata.

Ga dai abun da wasu daga cikin masu zaben ke cewa:

"Na zabi Tsipras kuma yanzu ma zan goyi bayan shi saboda ina rayuwa a Turai kuma na san 'yancin 'yan Turai da na Girka, ba daya ba ne, ba za'a iya kwatanta su ba, muna so mu kasance a cikin Turai, amma 'yancinmu ba daya ba ne shi ya sa."

Shi kuma wannan ya goyi bayan tayin Turan

"Ni na zabi a saboda na yi imani da demokiradiyya da kuma Hadin kan Turai, a duniyar da za ta kasance mai karfin tattalin arziki, kuma ina da sha'awar mu yi aiki tare don cigaba ba dan mayar da juna baya ba"

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a dai ya nuna cewa ra'ayoin masu goyon baya da marasa yi na kan-kan-kan.