Bakin haure da dama sun halaka yayin da har yanzu ake kokarin ceto wasu, sakamkon nutserwar jirgin ruwan da suke ciki a gabar ruwan Girka.
Jami'an ceto na gabar ruwan Girkan sun bayyana cewa, jirgin ruwan makare da bakin haure masu son shiga Turai ko tawacce hanya, ya nutse ne a yammacin Alhamis din wannan makon, inda har kawo yanzu akwai sauran mutane 90 da hadarin ya rutsa da su da ake kokarin ceto su, baya ga yara 27 da kuma wasu mata 11 da maza 52 da aka samu nsarar cetowa.