Girgizar kasa ta afkawa kasar Japan | Labarai | DW | 20.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar kasa ta afkawa kasar Japan

Labaran da ke shigo mana yanzu na cewar wata girgizar kasa mai karfin gaske ta afkawa wasu yankuna da ke kudu maso gabashin kasar.

Hukumomi a kasar suka ce karfin girgizar kasar ya kai maki 6.2 a ma'aunin richter kuma an gamu da wannan ibtila'i ne da misalin karfe biyar da mintuna arba'in agogon GMT.

Ya zuwa yanzu dai ba wani karin haske da aka samu dangane da asarar rai ko ta dukiya ko kuma jikkata a yankunan da lamarin ya wakana.