1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar ƙasa a ƙasar Burma

Charlotte Chelsom-PillNovember 11, 2012

Wata girgizar ƙasa mai karfin maki shidda da ɗigo shidda a ma'aunin rishta ta afkawa garin Mandalay da ke tsakiyar ƙasar Myanmar ko kuma Burma.

https://p.dw.com/p/16gk7
Hoto: dapd

Girgizar ƙasar dai ta yi ta'adi ga gine-gine da kuma jikkata mutane da dama a garin na Mandalay da kuma garin Shwebo da ke kusa.

A halin yanzu dai hukumomin Myanmar ɗin sakamakon girgizar ƙasar ta yi sanadiyyar rasuwar muatne biyu yayin da wasu guda biyar su ka ɓace.

A halin yanzu dai ma'aikatan ceto sun duƙufa wajen gano wanda su ka ɓata da kuma tallafawa wanda lamarin ya rutsa da su musamman ma dai a yankunan karkara.


Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar