Ginin sababbin matsugunai a Jerusalem | Labarai | DW | 07.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ginin sababbin matsugunai a Jerusalem

Isra'ila ta amince da gina wasu matsugunai na Yahudawa 'yan kama wuri zauna har 900 a gabashin birnin Jerusalem.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanjahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanjahu

Matakin dai ya biyo bayan wata shawara da Kwamitin tsara birane na Isra'ila ya yanke a wata tattaunawa da suka yi. Mai magana da yawun kwamitin Hagit Ofran ce ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun gabatar da bukata kuma an amince musu kana abunda ya rage shine su fara yin ginin matsugunan. Wannan sanarwa dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da mataimakin shugaban kasar Amirka Joe Biden ke yin wata ziyara a Isra'ilan. Ko da a watan Maris na shekara ta 2010 ma dai mahukuntan Isra'ilan sun sanar da aniyarsu ta gina matsugunan Yahudawan har 1,600 a birnin Ramat Shlomo da ke makwabtaka da birnin na gabashin Jerusalem.