Gidajen kallon kwallon kafa a Najeriya na fiskantar barazanar tashin bama-bamai | Zamantakewa | DW | 19.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gidajen kallon kwallon kafa a Najeriya na fiskantar barazanar tashin bama-bamai

Tun bayan da aka fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Brazil ake samun tashin bama-bamai a irin wadannan gidajen kallon, wadanda har suka kai ga hallakar rayuka.

Gasar kwallon kafa dai na da dimbin ma'abota a Najeriya ko da ko a wace nahiya ce, kuma daya daga cikin abubuwan da ke karawa wasan armashi shi ne idan ma'abota sun taru a gidan kallo guda, suna kallo cikin zumunci da walwala, suna tsokaci kan abubuwan da ke sosa musu rai dangane da wasar.

To amma yau an wayi gari ana fiskantar barazanar shudewar irin wadannan gidajen kallo saboda barazanar rashin tsaro.

Tuni ma wasu jihohin Najeriyar suka haramta irin wadannan gidajen kallon dan rage afkuwar irin wannan matsalar.

Ga dai rahotannin da muka hada kan wannan batu daga karkashin wannan shafin

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin