1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gibin albashin tsakanin 'yan siyasa da ma'aikata

Mohammad Nasiru Awal RGB
September 10, 2019

'Yan majalisun dokoki a kasashen Afirka da dama na samun albashi mai tsoka, yayin da suke cewa hakan na da muhimmanci, talakawa na korafin cewa akwai rashin adalci.

https://p.dw.com/p/3PMU0
Südafrika Kapstadt World Economic Forum
Shugabannin wasu kasashen Afirka yayin taron tattalin arziki a Afirka ta KuduHoto: AFP/R. Bosch

Rashin fayyace dalilan da ke sa ana karin albashin 'yan siyasar na kara janyo rashin yarda. A kasar Yuganda farashin kayayyakin masarufi na tashin gauro zabi, bisa wannan dalili ne 'yan majalisar dokokin kasar suka kara wa kansu albashi da kusan kashi 40 cikin 100, duk da cewa gababin karin, albashin 'yan majalisar ya ninka har sau 100 idan aka kwatanta da albashin da ma'aikaci ke karba a wata. 'Yan siyasa a wasu kasashen Afirka ma na kara wa kansu albashi a kai a kai.

Kenia Uhuru Kenyatta
Shugaba Kenyatta ya rage wa kansa albashi bayan kama mulkin KenyaHoto: imago/i Images

Su dai 'yan siyasa na cewa suna bukatar karin albashi saboda wasu ayyuka na jin dadin al'umma da tallafa wa jama'a da suke yi a mazabunsu. A Yuganda ga misali kowanne daya daga cikin 'yan majalisa su 459 na karbar albashi tsakanin Euro 3500 zuwa 7000 a kowanne wata bisa nisan mazabarsa da babban birni wato Kampala.

Nigerias Präsident Buhari und sein Vize beim APC-Parteitag
Najeriya na sahun gaba a karbar albashi mafi yawaHoto: Novo Isioro

Sai dai akwai wasu kasashen na Afirka da 'yan siyasa suka rage wa kansu albashi. Misali a kasar Burkina Faso, a shekarun baya 'yan majalisa sun rage yawan albashinsu da kashi 50 cikin 100. Shi ma shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta bayan nasarar zabe a 2017, ya sanar da rage wa 'yan majalisa da shi ma kanshi albashi da kashi 15 cikin 100. Sai dai har yanzu 'yan majalisa a Kenya na a sahun gaba wajen karbar albashi mafi yawa, sai kasar AfirKa ta Kudu da kuma Tarayyar Najeriya.