1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ghana ta kai karar Togo kan takaddamar iyakar Teku

February 20, 2026

Ghana na kokarin warware takaddama kan iyakar Teku a tsakaninta da Togo ta hanyar shari'a, bayan gazawar tattaunar shekaru takwas.

https://p.dw.com/p/59APf
Ghana Wahlen | John Mahama
Hoto: Seth/Xinhua/IMAGO

Ghana ta shigar da kara a gaban kotunan kasa da kasa domin warware takaddamar kan iyakar Teku da take yi da makwabciyarta Togo, saboda gaza samun daidaito a tsakanin bangarorin biyu bayan shafe shekaru takwas na tattunawa.

A cikin wata sanarwa da fadar mulki ta Accra ta fitar ta ce tun tuni ta sanar da Lomé cewa za a shata iyakar kasashen biyu bisa tsarin da yarjejeniyar dokokin Teku na Majalisar Dinkin Duniya ya tanadar.

Wannan mataki ya biyo bayan matakin shari'a da Ghana ta dauka a baya kan kasar Côte d'Ivoire, wanda kotun kasa da kasa ta yanke hukunci a 2017, lamarin da ke nuna yadda Accra ke neman tabbatar da tsaron iyakokinta na ruwa masu matukar muhimmaci ga tattalin arzikin kasar. 

Wadannan yankuna na gabar Teku da Ghana ke takaddama a kan su na da fadin dubunan kilomitoci kana kuma sun kunshi albarkatun danyen mai da kuma muhimman wuraren kamun kifi.