Ghouta: An fara isar da kayan agaji na jin kai | Labarai | DW | 05.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ghouta: An fara isar da kayan agaji na jin kai

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani ayarin motoci dauke da lodin kayan agaji ya isa a a garin Ghouta cibiyar 'yan tawayen Siriya, yayin da a daya bangaran ake ci gaba a yin barin wuta a kusa da birnin Damascus.

 Motocin wanda ke dauke da lodin kayan abinci da magunguna na mutane kamar dubu 27, Kungiyar Red Cross  ita ce ta shigar da shi. Wannan dai shi ne karo na farko da ake isar da agaji a Ghouta tun lokacin da yarjejeniya  tsagaita wutar da Rasha ta amince da ita ta fara aiki. Siriya dai na fama da yaki tun a shekara ta 2011 kuma kawo yanzu mutane dubu 340 suka mutu.