1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Taimakon IMF ga tattalin arzikin Ghana

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 28, 2022

Ministan kudi na Ghana Ken Ofori-Atta ya nunar da cewa, za a hanzarta cimma matsaya dangane da batun ceto tattalin arzikin kasar tsakanin gwamnati da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF.

https://p.dw.com/p/4HU8l
Ghana | Kudi | Tattalin Arziki
Tattalin arzikin Ghana na shirin shiga rudaniHoto: CC/bbcworldservice

Tuni ma dai wakilan asusun suka isa Ghana, tare da fara tattaunawa kan sauye-sauye da matakan da za a bi wajen samun rancen da mahukuntan Accra suka nema tun cikin watan Yulin wannan shekara. A cewar ministan kudi na Ghana Ken Ofori-Atta kawo yanzu ba su cimma kowacce irin yarjejeniya da asusun ba, yana mai cewa suna kokarin ganin an hanzarta tattaunawar ne saboda ceto tattalin arzikin kasar daga barazanar durkushewa. Ana dai sa ran jami'an asusun na IMF, za su kai har zuwa bakwai ga watan Oktoban da ke tafe domin tattauna batun da kuma ganin matsayin Ghana dangane da batun iya daukar bashin da kuma biyansa.