Ghana: Jawabin ban kwana na Shugaba Mahama | Siyasa | DW | 05.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ghana: Jawabin ban kwana na Shugaba Mahama

A ranar Asabar a birnin Accra za a yi bikin rantsar da sabuwar gwamnati karkashin sabon shugaban kasa Nana Akufo-Addo.

Shugaban kasar Ghana ya yi ganawar ban kwana da majalisar dokokin kasar wadda za a rusheta gabanin rantsar da sabon shugaban kasar a ranar Asabar. Ganawar tasa dai ta yi daidai da kundin tsarin mulkin kasar, wanda kuma a cikinsa ya sanar da ainihin halin da kasar ke ciki.

Da yake jawabin dai da ke zama na karshe Shugaba John Dramani Mahama ya mayar da hankali ne a kan wasu muhimman bangarori kama daga tattalin arziki, tsaro, kiwon lafiya, ababan more rayuwa, makamashi da kuma musamman ilimi wanda a cikin bayaninsa yake cewa:

"Za mu iya shaidar gagarumar bunkasar da bangaren ilimin kasar nan ya samu. A yanzu yara da dama ne ke samun 'yancin karatu tun daga tushe zuwa makarantun share fagen shiga jami'a, yadda bai taba kasancewa a tarihin sha'anin ilimin kasar nan ba."

Jim kadan bayan takaitaccen bayanan dai an samu mabambamtan ra'ayoyi daga bangarori daban-daban a gefen taron inda kuma na farko ke kasancewa daga ministar da ke kula da harkokin ilimi Farfesa Nana Jane Opoku Agyeman, wadda ta ce:

"Dukkan bayanansa ta fuskar bunkasa bangaren ilimin a bayyane suke kuma za a iya tabbatarwa a saukake. In ya ce an rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta haka yake, an samar da ingatattun littattafai a makarantu, wannan ma haka yake, da dai suaransu. Duk a bayyane suke."

Jakadan Amurka a Ghana Robert P. Jackson ya yaba da abinda ya kwatanta da halin dattaku da shugaban ya nuna inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

"Wannan lokaci ne musamman ga kasar Ghana a yayin da take shirin sauya gwamnati, kuma wannan damar na bai wa Mahama 'yancin zayyana aikinsa ta kyautu, kuma mataki ne da ya kamata al'ummar Ghana su yi alfahari da shi, duk kuwa da kalubalen da gwamnatinsa ta fuskanta. Shirin ya yi tsari kuma ina yi wa Ghana fatan alheri nan gaba."

Nana Akufo-Addo da ke jiran shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Ghana

Nana Akufo-Addo da ke jiran shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Ghana

Shi ma dai Twun Nuamah dan majalisar dokoki ne mai wakiltar mazabar Berekum kuma mamba ne a kwamitin gabatar da kudurorin kiwon lafiya a kasar, wanda kuma yayi tsokaci yana mai cewa.

"Akwai matukar takaici a yadda shugaban ke ci gaba da fakewa da wadannan bayanai ta fuskar kiwon lafiya, musamman a zantuttukan da suka danganci inshorar kiwon lafiya a yayinda a zahiri a kasa jama'a ba sa morarsa yadda ake tsammani. Saboda haka na so a ce ya zayyana ainihin matsalolin da akwai karara tare da bayyana matakan da za su ingiza gwamnati mai kamawa kan yadda za a lalubo bakin zaren warware shi."

Jama'a dai sun yaba da halin dauriya da dattaku da shugaban ya kwatanta musamman kiraye-kiraye da ya yawaita kuma ya sake maimatawa a kan muhimmancin hadin kan jama'ar kasar wajen zama tsintsiya madaurinki daya domin ciyar da kasar gaba ba tare da duba jam'iyya ba.

A karshen jawabin dai shugaba Mahama, ya ce Ghana bayan shugabancinsa za ta iya yin tinkaho da kanta a tsakanin wasu takwarorinta kasashen Afirka da ma duniya baki daya, musamman yin la'akari da yanayin tabarbarewar tattalin arziki da kasar take ciki a lokacin da gwamnatinsa ta amshi ragamar shugabancin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin