Ghana: Ana cigaba da kidayar kuri'u | Siyasa | DW | 08.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ghana: Ana cigaba da kidayar kuri'u

Hukumar zaben Ghana na cigaba da kidaya kuri'un zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa wanda aka gudanar ranar Larabar da ta gabata a fadin kasar.

Masu ruwa da tsaki a harkokin zaben na Ghana sun ce suna cigaba da kidaya kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa wanda fafatawa ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci John Mahama na jam'iyyar NDC da kuma babban mai hamayya dantakarar jam'iyyar NPP mai adawa Nana Akufo-Addo. Rahotanni sun bayyana cewa ana kidayar lami lafiya kuma ya zuwa yanzu ba wani labari daga hukumar zaben kasar kan wanda ke kan gaba a wannan kidaya da ake yi. A ranar Asabar din da ke tafe ne dai ake sa ran samun cikakken sakamakon. Idan har ba dan takarar da ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 to dole a tafi zagaye na biyu a zaben.

Sauti da bidiyo akan labarin