Ghana: An rantsar da shugaba Nana Akufo-Addo | Duka rahotanni | DW | 07.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Ghana: An rantsar da shugaba Nana Akufo-Addo

Sabon shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya yi alkwarin farfado da tattalin arzikin kasar da kuma samar da guraben ayyuka ga matasa.

A yau Asabar ne aka rantsar da sabon zababben shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a Accra babban birnin kasar.

Sabon shugaban mai shekaru 72 da haihuwa a jawabinsa bayan rantsar da shi ya yi alkawarin bullo da managartan matakai domin farfado da tattalin arzikin Ghana da kuma samar da guraben ayyuka ga matasa.

Bikin ranstuwar ya sami halaratar shugabannin kasashen 11 na Afirka da kuma tsoffin shugabannin kasar na baya da suka hada da , Jerry John Rawlings da kuma John Kufuor.


A cikin shekaru 25 da suka gabata dai, ana yi wa Ghana kallon kasa da ta kafa ginshikin dimokradiyya da kuma kwanciyar hankali a cewar daya daga cikin wadanda suka sa ido a zaben na cibiyar bunkasa demakaradiya ta NDI.