Gerhard Schröder tsohon shugaban gwamnatin Jamus ne. Shi ne ya yi sauye-sauye da suka baiwa kasarsa damar tayar da komadar arzikinta.
A shekarar 1944 aka haifi wannan jigo na jam'iyyar SPD da ya riki mukamin shugaban gwamnatin Jamus daga 1998 zuwa 2005. Shi ya kafa ginshikin rabuwa da makamashin nukiliya tare da rungumar makamashi mai tsabta.