1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gerhard Schröder A Kuwait

March 1, 2005

A balaguronsa ga kasashen Larabawa, shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya kammala ziyararsa ga kasar Kuwait ya kuma zarce zuwa Qatar

https://p.dw.com/p/Bvcw
Schröder da Bettermann na kaddamar da bikin bude tashar larabci ta Deutsche Welle
Schröder da Bettermann na kaddamar da bikin bude tashar larabci ta Deutsche WelleHoto: AP

Jim kadan bayan isarsa kasar ta Kuwait, shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder yayi Allah Waddai da hare-haren kunar bakin waken dake addabar kasar Irak a lokacin ganawarsa ta farko da P/M Kuwait. Dukkan jami’an siyasar biyu sun yi nuni da muhimmancin daukar nagartattun matakai domin murkushe wadannan hare-hare na ta’addanci. Daga bisani aka samu rahoton marabus din Karami, P/M kasar Lebanon da kuma zanga-zangar dubban daruruwan mutane a kasar. A lokacin da yake bayani a game da wadannan rahotanni da aka samu kakakin gwamnati Bela Anda cewa yayi:

Halin da ake ciki a kasar Lebanon tare da murabus din gwamnatinta abu ne dake nuna cewar sannu a hankali tsarin demokradiyya na samun gindin zama a kasar. A sakamakon adawa mai tsanani da ta fuskanta daga illahirin al’umar kasar, gwamnati, wacce kasar siriya ta sa baki domin nadinta, tayi murabus. Dukkan wadannan abubuwa ne dake yin nuni da alkiblar demokradiyya da al’umar Lebanon suka fuskanta yanzu haka.

Matsalar ta Lebanon ta shiga ajendar ganawar da shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi da magabatan kasar Kuwait. Babban dalilin haka kuwa shi ne kasancewar a zamanin baya-bayan nan rikice-rikicen dake faruwa a kasashen dake makobtaka ko kuma akalla suke kurkusa da ita su kan shafe ta kai tsaye, kamar yadda Bela Anda ya kara da bayani. Matsalolin na Lebanon da Iraki na daga cikin muhimman batutuwan da suka mamaye kanun labarai na farko da tashar Deutsche Welle ta gabatar a harshen larabci a fadar mulkin kasar ta Kuwait. Sabon sashen na larabci da aka kaddamar yana da ‚yan jarida 35 karkashin inuwarsa. An saurara daga bakin manajen-darekta na DW Erik Bettermann yana mai bayani a game da dalilin bude wannan sashe da aka yi inda yake cewar:

Manufarmu game da wannan tasha shi ne ba da gudummawa iya gwargwado a kokarin da ake na kyautata tuntubar juna tsakanin kasashen Larabawa da na nahiyar Turai, abin da ya hada har da Jamus. Musayar rahotanni na taka muhimmiyar rawa wajen kyautata fahimtar juna tsakanin jama'a. Kuma ba zata yiwu a sakarwa da kasar Amurka fage ta rika taka rawa ita kadai ba.

A kammala ziyarar tasa wadda ita ce ta farko da wani shugaban gwamnatin Jamus ya kai kasar Kuwait Gerhard Schröder zai halarci wasu bukuwa guda biyu, kafin ya zarce zuwa kasar Qatar, zangonsa na uku a balaguronsa ga kasashen Larabawa.