1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gazawar Afirka wajen magance matsalolinta

January 10, 2014

Rashin mulki na adalci da rashin shugabanci na gari da wasoso da dukiyar kasa suka janyo wa Afirka wannan masifa da take fama da ita.

https://p.dw.com/p/1AoZf
Hoto: picture-alliance/dpa

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wanda ta yi tsokaci a kan matsalar kabilanci a matsayin wata annoba a nahiyar Afirka.

Ta ce a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ana rikici tsakanin Kirista da Musulmi, a Sudan ta Kudu kabilun Nuer da Dinka na kashe juna. Gwamnatoci da hukumomi da dama a kasashen Afirka Kudu da Sahara sun yi matukar rauni ta yadda wani karamin gungun masu dauke da makami sun isa su tarwatsa kasa. Su kuma 'yan kasa ba za su iya kare kansu daga masu karbe mulki da karfi tuwo ba. Masu mulkin kuma ba sa tsinana wa talaka da komai, in ban da kuntata masa. Ba bambamcin addini ko kabila ne musabbabin rikice-rikicen da suka addabi nahiyar Afirka ba, rashin mulki na adalci da rashin shugabanci na gari da wasoso da dukiyar kasa suka janyo wa Afirka wannan masifa. Kasancewa babu mai iya dogaro ga sojoji ko 'yan sanda ko 'yan siyasa ko alkalai, bugu da kari ga rashin ababan more rayuwa, da zarar rikici ya barke sai kowa na koma wa ga 'yan kabilarsa ko mabiya addini guda da shi don samun tsira."

An kasa magance rigingimu a Bangui

Faransa ba za ta kara yawan dakarunta a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai mayar da hankali a kan rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa a wannan kasa.

Zentralafrikanische Republik französische Soldaten in Bangui 04.01.2014
Hoto: Miguel Medina/AFP/Getty Images

"Saboda tabarbarewar halin da ake ciki, Faransa ba ta da niyar tura karin dakaru Bangui. Aikin kwance damarar sojojin sa kai yana tafiyar hawainiya. Amma sojoji 1300 daga 1600 da Faransa ta girke a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya za su ci gaba da zama babban birnin kasar wato Bangui. Jaridar ta ce Faransa ta nunar da haka ne kwana guda gabanin taron kolin birnin N'Djamena babban birnin kasar Cadi a kan makomar shugaban rikon kwarya Michel Djotodia. Yanzu haka dai ana kara nuna shakku ko aikin samar da zaman lafiyar da sojojin Faransa ke yi zai yi nasara, kasancewa har yanzu ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a Bangui."

Kusantar juna tsakanin Al-Bashir da Kiir

Khartoum ta shiga taka sabuwar rawa, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai nuni da sha'awar shugaba Omar al-Bashir na daidaita al'amura a Sudan ta Kudu, sannan sai ta ci-gaba kamar haka.

Südsudan Sudan Omar al-Bashir bei Salva Kiir in Juba
Hoto: Reuters

"Rikicin Sudan ta Kudu ya sanya shugaban Jamhuriyar Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir sun fara kusantar juna. Bukatun bai daya game da sayar da man fetir da jajircewa sun sa tsoffin abokan gabar sun zama abokan dasawa yanzu. Jaridar ta ce a wannan mako gwagwarmayar neman rike madafun iko tsakanin shugaba Salva Kiir da abokin adawarsa Rike Machar ta bude sabon babi. Bayan ziyarar da ya kai birnin Juba shugaban Sudan al-Bashir ya yi wa takwaran aikinsa Kiir alkawarin ba shi cikakken goyon baya. Bisa ga dukkan alamu yanzu an manta da tsohuwar gaba da kuma zargin da ake wa gwamnatin Sudan na tsoma baki a harkokin cikin gidan Sudan ta Kudu."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu