1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yara na ci gaba da halaka a Zirin Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 20, 2024

Ma'aikatar Harkokin Tsaron Fararen Hula ta Zirin Gaza ta sanar da cewa hare-haren Isra'ila a birnin Tal al-Sultan da ke yankin kudancin Rafah, sun halaka mutane tara 'yan gida daya cikinsu har da kananan yara shida.

https://p.dw.com/p/4f0sP
Hari | Isra'ila | Zirin Gaza | Rafah
Sabon harin Isra'ila a birnin Tal al-Sultan da ke yankin kudancin Rafah ya halaka yaraHoto: Khaled Omar/Xinhua/IMAGO

Asibitin Al Najjar da ke birnin na Tal al-Sultan ya bayyana cewa yara biyar din da ke cikin mutanen da suka halaka a harin da Isra'ilan ta kai a yakin da take ci gaba da gwabzawa da kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza na Falasdinun, shekarunsu sun kama ne daga daya zuwa bakwai sai wata matashiya 'yar shekaru 16 a duniya da kuma mata biyu da magidanci guda daya. Cikin wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Tsaron Fararen Hular yankin Zirin Gazan Mahmud Bassal ya fitar, ya bayyana cewa an ciro mamatan ne a karkashin barakuzan gini bayan harin na Isra'ila da ta kai cikin daren da ya gabata.