1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Sojojin Isra'ila na shirin kwashe fararen hula

February 26, 2024

Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana shirinta na fara kwashe fararen hula daga yankunan da ake gabza fada a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4csRc
Rundunar sojin Isra'ila na son kwashe fararen hula daga Zirin Gaza
Rundunar sojin Isra'ila na son kwashe fararen hula daga Zirin GazaHoto: Ohad Zwigenberg/AP/picture alliance

Offishin Firanministan kasar Benjamin Netanyahu ya ce, rundunar ta mika shirinta na fara kwashe fararen hula daga Zirin Gaza a gaban kwamittin yakin. Sai dai babu wani karin bayani dangane da yadda za a kwashe fararen hula. Kwamittin yakin ya kuma amince da shirin kai kayayyakin agaji zuwa Zirin Gazan.

Wannan sanarwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ke shirin kai sabbin farmaki yankin Rafa, inda Falasdinawa kimanin miliyan 1.4 ke samun mafaka.

Har wayau, shugaban hukumar bayar da agaji ga Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, Philippe Lazzarin ya ce, kungiyar ta samu damar shiga da kayan agaji na karshe ne a ranar 23 ga watan Janairun wannan shekarar. A cewarsa, za a iya kaucewa fari idan har 'yan siyasa suka bada damar shiga da kuma kare kungiyoyin bada agaji a yankin.