Gaza kare mutane a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 01.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gaza kare mutane a Sudan ta Kudu

Bincike ya nuna dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun gaza kan kare fararen hula a Sudan ta Kudu.

Wani binciken Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu sun gaza mayar da martani bisa harin da sojojin gwamnati suka kai kan fararen hula. Binciken ya nuna an kai hari a waje mai nisan kasa da mil daya da sansanin dakarun kiyaye zaman lafiyar.

An daura alhakin haka kan rashin shiri, da rashin shugabanci na gari gami da tunanin abin da martanin zai haifar. Kasar ta Sudan ta Kudu ta fama cikin rikicin tun sabanin da ya kunno kai tsakanin Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar.