Gasar tseren keke a Kamaru | Zamantakewa | DW | 06.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gasar tseren keke a Kamaru

Dan Ruwanda mai suna Joseph Areruya ne ya lashe gasar tseren keke na 'yan Afirka da ke kasa da shekaru 23 da haihuwa bayan da aka shafe kwanaki hudu ana kece raini tsakaninsu, a kasar Kamaru

Wannan dai shi ne karon farko da hukumar tseren keke ta duiya ta shirya tseren keke na matasa zalla, da nufin bunkasa wnanan wasa a afirka. Kilomita 417 ne 'yan tseren keke da suka fito daga kasashe 15 na Afirka suka shafe daga ranar Laraba zuwa Lahadi tsakanin manyan biranen Kamaru biyu wato Yawunde da Douala. Dan Ruwanda mai suna Joseph Areruya ne ya lashe tseren da ake yi wa lakabi da Tour de Lespoir ko Tour of hope da Turanci. Dama dai shi Arearuya ne ya zo na daya a tseren Tropicale Amissa Bongo wanda ya fi kowanne suna a Afirka. Yayin da Jean Paul Ukiniwabo wanda shi dan Ruwanda ne ya zo na hudu. Dan Burkina Faso Paul Dumont kuma ya zo a matsayi na bakwai.