Gasar kofin zakarun nahiyar Afirka | Zamantakewa | DW | 18.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gasar kofin zakarun nahiyar Afirka

Kungiyar Mbabane Swallows daga Swaziland ta samu nasara ban-mamaki kan kungiyar AC Leopards ta kasar Kwango, a gaba daya da ci 4 da 3

Kuma da wannan nasara Mbabane Swallows ta zama wata kungiya ta farko daga Swaziland da ta kai wannan mataki na gaba. Haka ita ma kungiyar Zesco Utd daga Zambiya ta samu nasara kan Enugu Rangers daga Najeriya da ci 5 da 2 a gaba daya wasannin na gida da waje.

Anata bangaren kungiyar KCCA daga Yuganda ta samu nasara bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida a kan kungiyar Al Masry daga kasar Masar, da ci 4 da 3. Ita kuwa Mouloudia Alger daga Aljeriya ta yi sa'ar doke Young Africans daga Tanzaniya a gaba daya da ci 4 da 1.