1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka 2019

Mouhamadou Awal Balarabe
June 21, 2019

Kungiyoyi 24 za su fafata a gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afirka ta 2019 a Masar. Karon farko cikin tarihi da za a gudanar da gasar cin kofin na Afirka a lokacin bazara.

https://p.dw.com/p/3Kqdo
Nigeria Fußball-Nationalmannschaft, Ahmed Musa
Hoto: Getty Images/AFP/I. Kington

Ba a taba yin shirye-shiryen gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka cikin sarkakiya kamar a wannna karon ba. Da farko kamaru ta gaza shirya gasar cikin wa'adin da aka kayyade mata, lamarin da ya sa aka janye daukar bakuncin gasar daga hanunta a karshen watan Nuwamba 2018 saboda jinkirin gina filaye kwallo da ababen more rayuwa.

A farkon watan Janairu ne, aka zabi Masar a matsayin mai maye gurbinta. Sannan kuma tsibirin Komoros ya shigar da kara gaban Kotun duniya da ke hukanta lamuran wasanni domin a dakatar da kasar Kamaru saboda bai kamata ta ci bulus bayan gaza shirya gasar ta Afirka ba. Amma kuma hakarta ba ta cimma ruwa ba. Bugu da kari kuma a farkon watan Yuni, makonni biyu kafin a fara gasar, an kama shugaban hukumar kwallon kafar Afirka Ahmad Ahmad a otel a Paris don amsa tambayoyi game da zargin cin hanci da rashawa.

Fußball | Africa Cup 2017 | Togo vs Elfenbeinküste
Togo da Ivory Coast a lokacin gasar 2017Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wannan dai shi ne karon farko cikin tarihi da za a gudanar da gasar cin kofin Afirka a lokacin bazara. Sai dai tsohon dan wasan Tunisiya Zoubair Baya wanda ya taba bugawa a Freiburg na Jamus ya ce 'yan wasa za su fuskanci kalubale iri-iri.

Wani ci gaba da aka samu a gasar kwallon kafar Afirka shi ne samun kasashe 24 da za su fafata tsakaninsu sabanin baya inda ake samun kasashe 16. Wannan yana nufin cewar wasu daga cikin kasashen da za su zo na uku a rukunoninsu za su iya samun cancantar shiga zagaye na gaba, kamar yadda yake wakana a gasar zakarun Turai. Ko da yake wasu kwararru a harkar kwallon kafa na ganin cewar wannan tsari zai cire wa gasar amarshi, amma Patrick Mboma tsohon dan wasan Indomitable Lions na Kamaru ya ce ba kasar da za ta yi sake ballatana a yi mata sakiyar da ba ruwa.

Fußball Nationalspieler Mahmoud Hassan Trezeguet
Hoto: picture-alliance/empics/G. Barker

 A 2017 Kamaru ta lashe gasar Afirka da daya daga cikin kungiyoyi mafi raunin na tarihin kwallon kafarta. Amma baya ga ita, kasashe uku ne ake hasashen cewa za su iya taka rawar gani ciki har da Masar da ke daukar bakuncin gasar da Senegal da ta kunshi fitatun 'yan wasa irin su Kalidou Koulibaly da ke bugawa a Naples, da Sadio Mané na Liverpool. Sai dai kuma Moroko wacce baya ga gogaggun 'yan wasa, ke da mai horaswa Hervé Renard wanda ya nasarar lashe gasar sau biyu tare da kungiyoyi biyu dabam-dabam. Sai dai tsohon dan wasan Tunisiya Zoubaier Baya ya ce Aljeriya za ta iya bai wa mara da kunya.

Najeriya da Ghana ma za su iya kai bantensu a wannan gasa, ko da shi ke suna fuskantar matsaloli da dama kama daga bangaren 'yan wasa har izuwa ga bangaren shugabanni