Gargadin sojojin Masar ga masu bore | Labarai | DW | 14.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gargadin sojojin Masar ga masu bore

Gwamnatin kasar Masar ta jaddada aniyarta ta sa kafar wando guda da masu boren yin Allah wadai da juyin mulkin matikar suka ci-gaba da gurganta harkokin sufuri.

Ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Masar ta fitar da wata sanarwa a ranar Asabar, wadda a ciki ta yi kashedi tare da shan alwashin dakile daukacin masu boren da ke janyo tsaiko ga ababen hawa a sassa daban daban na kasar. Wannan sanarwar dai ta fito ne yini daya kacal bayan da dubbannin masu zanga zanga suka yi gangami a Alkahira babban birnin kasar ta Masar, domin yin Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi wa zababbiyar gwamnatin farar hula a karkashin shugaba Mohammed Mursi a ranar uku ga watan Yulin da ya gabata.

Hakanan sanarwar gwamnatin ta zargi masu zanga zangar da aikata laifuka daban daban, da suka hada da katse hanyoyi da sace 'yan jarida da kuma kwace wasu daga cikin na'urorinsu. Sai dai kuma mambobin kungiyar 'Yan Uwa Musulmi sun sha alwashin ci-gaba da gudanar da zanga-zangar lumana a kowane mako, domin nuna adawarsu ga matakin da sojojin suka dauka na kifar da gwamnatin demokaradiyyar kasar.

Mawallafi: saleh Umar saleh
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe