Gargadin Putin ga Obama a kan Syriya | Labarai | DW | 12.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gargadin Putin ga Obama a kan Syriya

Shugaban Rasha Vladmirin Putin ya ja hankali takwaran aikinsa na Amirka Barack Obama kan illar da ke tattare da afkawa Syriya da yaki a fannin zaman lafiya a duniya.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gargadi Amirka da ta guji daukan matakin soji a kan gwamnatin Bashar al-Assad na Syriya, idan ta na so a samu zaman lafiya a tsakanin kasashen duniya. Sakon na Putin na kunshe ne cikin wani sharhi da ya rubuta a jaridar New York Times, inda ya ce duk wani hari da Amirka za ta kai wa Syriya zai iya bude wani sabon babi na hare-haren ta'addanci tare da yin karar tsaye ga zaman lafiya.

Shugaban Na Rasha ya kuma soki lamirin Amirka inda ya ce mutane da dama a duniya ba sa daukanta a matsayin wani abin misali a fuskar demokaradiya da kuma kare hakkin bil Adama. Amma maimakon haka, suna yi mata kallon mai amfani da tsinin bindiga wajen tabbatar da angizonta a duniya.

Matsayin da Putin ya bayyana ya na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da kuma ministan harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov ke tattaunawa tsakaninsu a birnin Geneva na Switzerland ko Suisse. Babban abin da sassa biyu suka sa a gaba dai shi ne tantance hanyoyin da za a bi wajen karbewa ko kuma killace makamai masu guba da gwamnatin Bashar al-Assad ta mallaka.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu