Gargadi wa kasashe dake makwabtaka da Turkiyya kan Murar tsuntsaye | Siyasa | DW | 11.01.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gargadi wa kasashe dake makwabtaka da Turkiyya kan Murar tsuntsaye

Cutar murar tsuntsaye a Turkiyya

Cutar murar tsuntsaye a Turkiyya

Hukumomin kula da lafiya a Turkiyya sunyi gargadin yiwuwar bartkewar annobar murar tsuntsaye tsakanin jamaa dama kasashe dake makwabtaka da ita,duk da matakai da aka dauka.

Kwararru ta fannin kula da lafiyan dabboni na mdd sunyi gargadin cewa kwayar cutar murar tsuntsye ta H5N1 data kashe matasa biyu a turkiyya na iya zama babbar barazana ga wasu kasashen dake makwabtaka da ita.

Duk da matakan da aka dauka na kare yaduwar kwayoyin cutar ,wanda suka hadar da kashe dukkan kajin dake yankunan da abun ya shafa,akwai barazanar yaduwar cutar zuwa wasu yankuna dake kewaye,inji hukumar kula da abinci ta mdd.

Babban jamii a hukumar kula da dabbobi na mdd Juan Lubroth ya bayyana cewa idan baa dauki tsauraran matakai fiye da na baya ba yaduwar cutar tsakanin mutane da dabbobi zaiyi barazana a wuraren da wannan cuta ta bulla dakuma inda har yanzu ana cigaba da bincike.

A yau dai hukumomin kula da lafiya a turkiyyan sun hakikance cewa sun dauki matakai na kariya bayan tabbatar da cewa ana jinyan mutane 13 da suka kamu da ita,sakamakon mutuwan yara matasa biyu daga cutar a yankin kudu maso yammacin kasarr a makon daya gabata.

Wadannan yara biyu da suka gamu da ajalinsu ta murar kajin dai sune na farko wajen kudancin Asia da Sin ,inda cutar ta fara bulla a shekaru 2 da suka gabata kuma ta hallaka mutane sama da 70.

Directon turai na hukumar kula da lafiya ta mdd Mark Danzon,ya yabawa yadda hukumomin turkiyyan suka dauki matakai na gaggawa na shawo kan lamarin.

Inda ya kara dacewa

Dole ne mu tashi tsaye wajen gudanar da campaign din ilimantar da jamaa dake dukkan kasashe,kancewa idan sunga kajinsu na fama da rashin lafiya ko suna mutuwa kada su tabasu,kana su gaggauta kashe sauran kaji da makamantansu dake yankin.

Mutane zasu iya kamuwa da murar tsuntsaye ne daga dabbobi dake dauke da kwayar cutar,amma masana kimiya sun bayyana cewa miliyoyin mutane zasu iya gamuwa da ajalinsu daga cutar idan ta saje da murar da biladama kanyi ,wadda kuma kan yadu tsakanin mutane cikin gaggawa.

Hukumar kula da abinci ta mdd wadda ta aike da kwararrun likitocinta Turkiyya tayi kira ga kasashen Armenia da Azerbaijan da Georgia da Iraki da Iran da Syria dake makwabtaka dasu dauki matakai na wayar dakan alummominsu akan illolin wannan cuta ta zazzabin murar tsuntsaye da matakan kariya.

 • Kwanan wata 11.01.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu2X
 • Kwanan wata 11.01.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu2X