1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadi kan fadada shirin nukiliyar Iran

Ahmed SalisuMarch 30, 2015

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce bai kyautu a bar Iran ta fadada shirinta na nukiliya cikin hanzari ba saboda irin hadarin da haka ke da shi.

https://p.dw.com/p/1Ezlt
Iran IAEA Inspektion in Natanz 2014
Hoto: Imago

Steinmeier ya ce ko kusa bai kamata a ce sun bar Tehran ta samu wani cigaba mai yawa cikin shekaru goma da ke tafe ba a shirin na ta da ke cike da takaddama.

Kalaman na ministan harkokin wajen na Jamus na zuwa daidai lokacin da ake cigaba da tattaunawa don cimma matsaya kan wannan batu wanda wa'adin hakan ke cika a tsakar daren yau.

Shirin na nukiliyar Iran dai na shan suka saboda zargin da ake yi na cewar ta na yinsa ne da nufin samun makamin kare dangi, zargin da ta sha musantawa har ma ta kan ce ta na yin sa ne da nufin samar da makamashi.