Gangamin kin ta′addanci a Spain | Labarai | DW | 25.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gangamin kin ta'addanci a Spain

Shugabar birnin Barcelona na Spain Ada Colau ta yi kira ga al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu a wannan Asabar don gudanar da gangami na nuna adawa da ayyukan ta'addanci.

Shugabar ta yi wannan kiran ne biyo bayan hare-haren da aka kai a yankunan biyu a makon jiya da ya salwantar da rayukan mutane goma sha hudu, Colau ta bukaci al'umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu a wannan Asabar don gudanar da gangami na nuna adawa da ayyukan ta'addanci, Colau ta ce ya na da mahinmanci al'umma su sani cewa ba za su yi rayuwarsu cikin fargaba ba duk kuwa da barazanar da kasar ke fuskanta daga masu tsatsaurar ra'ayi.

Sarki Felipe da Firaiminista Mariano Rahoy tare da wasu manyan 'yan siyasar kasar za su jagoranci gangamin a wani abu da ke hada kan 'yan kasar bayan rudanin da kasar ta fada a sakamakon harin ta'addanci da kungiyar IS ta kai a wurin shakatawa da akasari baki ke yawan zuwa, jami'an tsaro sun dauki akalla mako suna farautar wadanda ake zargi da kitsa harin, an kuma tabbatar da kashe mutumin da aka ce shi ya tuka wata babbar mota a cikin jama'a a harin na Barcelona.