Gangamin dubban mutane a Abuja | Siyasa | DW | 30.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gangamin dubban mutane a Abuja

Kungiyoyin mata suka kira wannan gangamin don kara yin kira ga gwamnatin Najeriya ta hanzarta daukar kwararan matakan ceto mata 'yan makaranta a Chibok.

Duk kuwa da ruwan saman da aka yi a babban birnin na Najeriya, dubban mata da kungiyoyin da ke rajin kare hakin jama'a sun yi zanga-zanga, domin kara matsin lamba ga gwamnatin Najeriyar ta hanzarta ceto 'yan matan nan sama da 200 da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a daga wata makarantar sakandare ta 'yan mata da ke agarin Chibok na jihar Borno.

Masu zanga-zangar sun nuna bacin ransu a matsayinsu na iyaye mata da rashin kazarkazar da suke gani daga bangaren hukumomin Najeriya.

Hajiya Hadiza Bala Usman ita ce jami'ar kula da tsara wannan zanga-zanga ta ce tura fa ta kai bango shi yasa suka kai ga fitowa kan titi.

"Abinda muke so shi ne al'ummar Najeriya gaba daya ta fito haikan ta nuna cewa ba za ta yarda a ce yara sun bace ba babu wani bayani ba. Dole ne mu fito mu nuna wa hukuma cewa ba yadda za a ce an maida rai ba bakin komai ba, in an kashe mutum ko an sace shi sai a juya a ci gaba da harka kawai, haka ba zai yiwu ba."

Matan dai da wasu daga cikin mazajen da suka yi gangamin sun sanya jajaye riguna da hulunna "hana Sallah" domin nuna juyayin bakin cikin halin da ake ciki, musamman rahotani da ke cewa an ma fice da 'yan matan zuwa wasu kasashe.

Fatan da ake shi ne karin matsin lamba irin wannan ya tilasata wa gwamnatin sauya salonta a kan wannan lamari da ke ci gaba da zama babban kalubale da har wasu ke ganin gazawa ce a fanin mahukuntan Najeriyar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin