Ganawar Shugaba Abbas da Premier Haniya na Palasdinawa | Labarai | DW | 15.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Shugaba Abbas da Premier Haniya na Palasdinawa

Shugaba Mahmood Abbas na yankin palasdinawa da prime minista Ismael Haniya na gudanar da wata tattaunawa ta keke da keke a zirin Gaza ,da nufin kawar da sabanin dake neman yin karan tsaye adangane da kafa gwamnatin hadin kann yankin dake neman cin tura.Wannan tattaunawa tazo ne ayau a ofishin shugaba Abbas ,jim kadan da zuwan shugaban daga babban ofishinsa dake gabar yamma da kogin Jordan ,cikin matukar damuwan cewa Amurka bazatayi laakari da sabuwar gwamnatin yankin ba.Abbas wanda a makon daya gabata ya cimma yarjejeniya da Hamas a dangane da kafa gwamnatin hadaka ,kungiyar da kasashen turai suka jera cikin na taadda,tunda farko ya gana da jakadan Amurka General Jacob Walles a birnin Ramallah.