Ganawa tsakanin Solana da Larijani a Brussels | Labarai | DW | 11.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawa tsakanin Solana da Larijani a Brussels

A takaddamar nukiliya da ake yi da Iran, a yau za´a gana tsakanin babban jami´in harkokin ketare na KTT Javier Solana da babban mai shiga tsakani a tattaunawar nukiliya gwamnatin birnin Teheran Ali Larijani a birnin Brussels. Ganawar ta yau za ta mayar da hankali akan tayin taimakon da gamaiyar kasa da kasa ta gabatar da nufin gano bakin zaren warware wannan takaddama. Ga ra´ayin gwamnati a Teheran dai akwai abubuwa masu daure kai a wannan tayi wanda za´a tattauna kai a taron na birnin Brussels. Tayin wanda kasashen biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu da kuma Jamus suka bayar ya tanadi bawa Iran taimakon tattalin arziki da na siyasa idan kasar ta yi watsi da shirin ta na inganta sidanarin uranium. Tun da farko Iran ta nunar da cewa a cikin watan augusta zata ba da amsa ga wannan shawara.