Gambiya: Za a fafata a zaben ′yan majalisar dokoki na wannan Alhamis | Labarai | DW | 05.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gambiya: Za a fafata a zaben 'yan majalisar dokoki na wannan Alhamis

'Yan Gambiya sama da budu 886 za su kada kuri'ar zaben 'yan majalisar dokoki mai kujeru 58 daga cikin 'yan takara 238 da suka fito daga jam'iyyun siyasa tara da kuma masu zaman kansu.

A wannan Alhamis ce al'ummar Gambiya ke kada kuri'ar zaben 'yan majalisar dokokin kasar. Mutane sama da dubu 886 ne da suka cancanci kada kuri'ar tasu daga cikin kasa da mutane miliyan biyu da kasar ta kunsa, za su kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin kasar daga cikin 'yan takara 238 da suka fito daga jam'iyyun siyasa tara da kuma masu zaman kansu. 

Majalisar dokokin Gambiyar dai na kunshe ne da mambobi 58, sai dai a karkashin dokokin kasar, shugaban kasa ne ke da hurumin nada biyar daga cikin wadannan 'yan majalisar a wa'adin shekaru biyar. 

Wannan dai shi ne zaben 'yan majalisar dokoki na farko da kasar ta Gambiya za ta shirya tun bayan kawo karshen mulkin shekaru 22 na Shugaba Yahya Jammeh wanda yanzu haka yake zaman gudun hijira a kasar Equatorial Guinea, tun bayan da ya sha kayi a gaban Adama Barrow a zaben watan Disambar shekarar bara da ya kasance mai cike da cece-kuce.