Gambiya ta shiga mawuyacin hali | Siyasa | DW | 18.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gambiya ta shiga mawuyacin hali

An gabatar da kudirin Majalisar Dinkin Duniya ta amince da amfani da karfi a Gambiya domin kawo karshen Shugaba Yahya Jammeh jim kadan bayan majalisar Gambiya ta amince da shirin tsawaita wa'adin Jammeh da watanni uku.

Kasar Senegal ta nemi Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da matakin amfani da karfi karkashin kasashen ECOWAS domin kawo karshen gwamnati Shugaba Yahya Jammeh na Gambiya wanda wa'adinsa yake kawo karshe 19 ga watan Janairu.

Haka yana zuwa yini guda bayan majalisar Gambiya ta amince da shirin tsawaita wa'adin Shugaba Jammeh da watanni uku kuma kwana guda kafin rantsar da sabon zababben shugaban Gambiya Adama Barrow. Rahotanni sun ce tuni sosojin Senegal suka isa kan iyaka da Gambiya yayin da Najeriya ta tura jirgin ruwa na yaki.

Shugaba Jammeh ya sanar da dokar ta bacin ta watanni uku a fadin kasar, a yunkurinsa na ci gaba da rike madafan iko duk da kaye da ya sha a zaben watan Disamba.

Tuni dai sabon zababben shugaba Adama Barrow ya lashi takobin kama ragamar mulki a gobe Alhamis, tare da goyon bayan hukumomin kasa da kasa.

Da wannan sabon rikici dai baki da ma al'ummar kasar ta Gambiya na ci gaba da ficewa, galibi zuwa Senegal ko kuma Guinea Bissau.

Sauti da bidiyo akan labarin