Gambiya ta matsa a kan binciken Yahya Jammeh | Siyasa | DW | 27.12.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gambiya ta matsa a kan binciken Yahya Jammeh

Ministan shari'a a Gambiya, ya bukaci da a yanke wa tsohon Shugaba Yahya Jammeh da mukarrabansa hukunci sakamakon mulkin da kama-karya da suka yi tsawon shekaru 22.

Gambia Ex-Präsident Yahya Jammeh

Tsohon shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh

Kiran na zuwa ne bayan da aka bayyana sakamakon binciken da hukumar Bincike da sasantawa da biyan diyya ta kasar TRRC da aka kafa domin banciko yadda Jammeh ya gudanar da mulkinsa tsakanin shekarun 1996 zuwa 2017.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne dai hukumar ta bayyana sakamakon binicken da ta yi ga al'ummar kasar ta Gambiya, bayan da ta kwashe tsawon shekaru uku tana gudanar da bincike kan mulkin na tsohon shugaban Gambiyan Yahya Jammeh da mukarrabansa.

An dai bayyana cewa suke da alhakin kisan Kajali Jammeh da Yamma Colley da Bai Dam da Sheikh Faal Pa Ous Jeng da kuma wsu utane uku da ake kyautata zaton makiyaya ne.

Baya ga haka kuma Jammeh ne ke da alhakin kisan gilla ga Ceesay Bujiling. An kuma alakanta shi da aikata muggan laifuka da dama tun daga watan Yulin 1994 zuwa Janairun 2017. Laifukan sun hadar da kashe wasu sojoji 11 a 1994 da kisan ministan kudi na Gambiya a 1995 da kisan wasu fararen hula 17 a watan Afrilun 2000 da kisan wasu 'yan ci-rani mafi yawan su daga kasar Ghana su sama da 50. Sainabou Lowe ta bayyana cewa dan uwanta Ebou Lowe na daga cikin sojojin da aka kashe a shekara ta 2006, bayan juyin mulkin da aka yi yunkurin yi wa Jammeh da bai yi nasara ba.

Senegal Daka 2005 | Yayah Jammeh, Präsident Gambia & Abdoulaye Wade, Präsident

Tsohon shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh

Yahya Jammeh ne dai ke da alhakin cin zarafin wasu 'yan jaridar Gambiya, ta hanyar tirsasawa da muzgunawa da azabtarwa. Dan jarida Ebrima Manneh ya yi batan dabo, tun a shekara ta 2006 yayin da Jammeh ya sa aka halaka Deyda Hydara a 2004. Sana Camara dan jarida ne da aka cafke, kafin daga bisani ya yi gudun hijira.

Gwamnatin ta Jammeh dai ta ci zarafin mata ta hanyar fyade, Fatou Jallow na daga cikin matan da aka ci zarafinsu da kuma ta bayar da shaida a gaban kwamitin. Fatou Baldeh mai fafutukar kare hakkin mata ce a Gambiyan.

Lamin Tamba magoyin bayan Jammeh ne, kuma a cewarsa kundin tsarin mulkin Gambiya na yanzu ya bai wa Jammmeh kariya.

Reed Brody na Hukumar Alkalai ta Kasa da Kasa, ya bayyana cewa lokaci ya yi da gwamnatin Gambiya za ta hukunta Jammeh. Tsohon mai fafutikar kare hakkin dan Adam din ya ce, akwai bukatar gwamnatin ta gaggauta bi wa wadanda aka zalunta hakkinsu, kuma an saka idanu daga ciki da wajen kasar. A cewarsa ba abin mamaki ba ne ganin Jammeh ya fuskanci wadanda ya zalunta a otu nan ba da jimawa ba. Gwamnatin dai na da tsawon watanni biyar, ta bayyana matsayarta da kuma daukar mataki kan binciken kwamitin.

Sauti da bidiyo akan labarin