Gambiya: Paracetamol na illata yara | Zamantakewa | DW | 20.09.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gambiya: Paracetamol na illata yara

Hukumar Lafiya ta Gambiya ta dakatar da amfani da maganin Paracetamol na ruwa wanda aka saba amfani da shi wurin rage radadin ciwo ga yara a kasar, biyo bayan mutuwar yara da dama tare da jikkata wasu.

Gambiya | Yara | Illa | Paracetamol | Magani

Kananan yara na fuskantar matsaloli sakamakon maganin Paracetamol na ruwa

Jami'an lafiya sun nunar da cewa yawan ciwon koda da ya mamaye kasar a kwanakin baya-byan nan, na da nasaba da illar wannan maganin. A dangane da haka ne aka dakatar da shan maganin har sai yaanda ta yi wu, koda yake an amince a yi amfani da kwayoyin Paracetamol din. Wata kungiya da ke kare hakkin yara ta Child Protection Alliance, ta bayana mutuwar yaran a matsayin abin jimami ga kasar baki daya. Kungiyar na kuma fatan wannan ya zama tuni ga hukumomi a kan ayyukansu na kare yara da bunkasa rayuwarsu a fannoni dabam-dabam. Hukumamin kiwon lafiya na Gambiyan dai na fatan dakatar da amfani da maganin ba zai dauki lokaci ba, wanda hakan zai dogara ne kawai da sakamakon binciken da aka samu.

 

Sauti da bidiyo akan labarin