1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya: Jammeh ya nada mai shiga tsakani

January 11, 2017

Tawagar ECOWAS wadda ke shiga tsakanin don shawo kan Yahya Jammeh ya mika mulki ta jinkirta zyarar da ta shirya kaiwa don ganawa da Jammeh bayan da shugaban ya bukaci a kara masa lokaci.

https://p.dw.com/p/2VdCv
Elfenbeinküste Präsident Yahya Jammeh in Yamoussoukro
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Shugaban Gambiya mai barin gado Yahya jammeh ya nada mai shiga tsakani wanda zai tattauna a madadinsa da shugaba mai jiran gado Adama Barrow.

Jammeh wanda ya yi mulkin kasar tsawon shekaru 22 ya ki amincewa da shan kaye a zaben da ya gudana na ranar 1 ga watan Disamba.

Sakataren Jam'iyya mai mulki zai shiga tsakani domin tattaunawar cimma masalaha kan takkamar siyasar.

A waje guda shugabannin kasashen yammacin Afirka da ke shiga tsakani domin sulhunta rikicin siyasar Gambiya sun jinkirta ziyarar da suka shirya kai wa zuwa Gambiya a wannan makon bayan da shugaba Yahya jammeh ya bukaci su kara masa lokaci.

A cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban Najeriya ya sanyawa hannu yace ko da yake shugabanin sun jinkirta ganawar da za su da Jammeh, suna nan akan bakan su cewa wajibi ne Jammeh ya martaba kundin tsarin mulkin kasar.

A yau laraba ne aka shirya shugabanin na ECOWAS da suka hada da Muhammdu Buhari na Najeriya da Ellen Johnson Sirleaf ta Liberiya da tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama za su je Banjul domin matsawa Yahya jammeh ya martaba sakamakon zaben kasar da aka gudanar na ranar 1 ga watan Disamba, ya sauka cikin mutunci a karshen wa'adin mulkinsa.