Gagarumar zanga-zanga a Burkina Faso | Labarai | DW | 28.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gagarumar zanga-zanga a Burkina Faso

Dubban masu adawa da yunkurin yin tazarce ne suka yi taho-mu-gama da jami'an 'yan sanda a Burkina Faso a kokarin da 'yan sandan suka yi na tarwatsasu da karfin tuwo.

'Yan sandan dai sun harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zangar a yayin da suka tunkari majalisar dokokin kasar. Al'amarin ya faru ne bayan da masu adawa da yunkurin shugaba na yin tazarce suka yi fitar dango a Ouagadougou babban birnin kasar, suna masu yin kira ga shugaba Blaise Compaore da ya sauka daga kan mukaminsa sakamakon mika bukatar yin gyara a kundin tsarin mulki da ya ke kokarin yi ga majalisar dokoki.

Shugaba Compaore dai na son yin kwaskwarima ga fannin wa'adin zama kan karagar mulki domin samun damar yin tazarce a kan kujerar shugabancin kasar duk kuwa da cewa wa'adin mulkinsa ya cika. Compaore ya kasance jagaba a wajen sulhunta rikici a nahiyar Afirka inda kuma ya ke zaman babban abokin burmin kasashen yamma kasancewar ya na basu goyon baya a yakin da suke da kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qa'ida.