1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin lafiyar Ali Bongo ta janyo matanin 'yan siyasa

Abdourahamane Hassane
August 12, 2019

Nan gaba a ranar 26 ga wannan wata wata kotu a Gabon za ta saurari wani karan da 'yan adawar kasar suka shigar na neman a gudanar da bincike na kiwon lafiya a kan Shugaba Ali Bongo Odimba.

https://p.dw.com/p/3Nn7w
Gabun Ankunft Präsident Ali Bongo in Libreville
Hoto: Getty Images/AFP/S. Jordan

'Yan adawar suna neman da a gudanar da binciken ne domin tantance ko shugaban na Gabon yana iya ci gaba da yin mulkin. Watannin goma tun bayan da shugaban na Gabon ya samu mutuwar rabin jiki, bai taba yin wani jawabi ko wata sanarwa ba. Ali Bongo wanda ke kan mulki tun mutuwar mahaifinsa Omar Bongo a shekara ta 2009 ya fadi da rashin lafiya a lokacin da yake yin wata ziyara a Saudiya a shekara ta 2018.