Gabashin birnin Kudus babban birnin Falasdinu | Labarai | DW | 13.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gabashin birnin Kudus babban birnin Falasdinu

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga kasashen duniya da su aminci da gabashin birnin Kusdus a matsayin babban birnin Falasdinu.

Recep Tayyip Erdogan ya yi wannan kira ne a wajen taron kungiyar kasashe Msulmi OIC ko kuma  OCI da ke gudana a birnin Istanbul. Sai dai a halin da ke ciki  kasashe da dama na Musulmi ba sa son yin ja in ja da Amirka da kuma ma Isra'ila. Amma dai tuni da kasashen Iran da Jodan da Qatar da Libanon da kuma Sudan wadanda shugabanninsu ke halarta taron suka amsa kira na shugaban Turkiyya.