G5 Sahel: Taron magance rikicin ta′addanci | Siyasa | DW | 01.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

G5 Sahel: Taron magance rikicin ta'addanci

An gudanar da wani taro a Jamus a game da hanyoyin da za a bi domin ganin bayan rikicin ta'addanci a kasashen yankin Sahel. Mahalarta taron sun hada da wakilai na kasashen Burkina Faso da Nijar da Mali da kuma EU.

Kasashen yankin Sahel sun samu kansu cikin wani hali na rashin tabbas a sakamakon karuwar hare-hare na ta'addadnci a kan fararen fula da kuma jami'an tsaro a Burkina Faso da Mali da  kuma Nijar. Daman dai Jamus da sannu a hankali tana kara kasancewa cikin wasu kasasahen na yankin sahel ta hanyar aiyyukan raya kasa da kuma yaki da ta'addanci. A muhawarar da kwararru da malaman jami'oi suka kwashe dogon lokaci suna tafkawa, sun ambato matsaloli daban-daban da ke ke ci wa yankin na Sahel tuwo a kwarya da ya hana karya lagon ta'adda.

Dukkanin kwararun sun yi amanar cewar talauci da rikicin filaye a sakamakon canjin yanayi da ake samu da kuma  jahilci na daga cikin abin da suka kara assasa aiyukan ta'addanci a yankin da kuma matsalar rashin aikin yi na matasa. Misali dai a Mali yawancin masu aiyyukan na ta'addanci matasa ne wadanda suka rasa abin yi saboda gwamnatin ta gaza cika musu burinsu na ba su aikin yi.

An yi  ta kai ruwa rana tsakanin wakilan Kungiyar Tarrayar Turai a taron wacce ke bai wa kasashen na yakin Sahel tallafi na tsaro  da raya kasa abin da wasu suke ganin duk da dauki na EU, babu wani ci gaba da aka samu, ko da yake wakilin na EU ya ce an samu dorewar mulkin demokaradiyar a yankin.Makasudin taron dai shi ne na samar da wasu hanyoyi bai daya domin tinkarar  lamarin ta'addanci a yankin Sahel ta hanyar amfani da shawarwari a tsakanin kungiyoyin farar fula na yankin Sahel da na Turai.

 

Sauti da bidiyo akan labarin