Fursunoni sun yi tashin hankali a Brazil | Labarai | DW | 02.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fursunoni sun yi tashin hankali a Brazil

Jami'an 'yan sanda sun tabbatar da mutuwar fursunoni tara tare da jikkata wasu 14, bayan barkewar rikici a gidan yarin da ke Jihar Goiania.

Rikicin ya barke ne bayan da wasu gungun fursunonin dauke da makamai suka kutsa dayan bangare suka cillawa katifu wuta, tare da fille kan wani. Jami'an tsaron gidan yarin sun tabbatar da tserewar sama da fursunoni 100, sai dai an yi nasarar kama wasu. Wannan dai ba shi ne karon farko ba  da ake samun rikita-rikita a gidajen yarin Brazil , inda ko a bara sai da wasu fursunoni suka ba hamata iska abin da ya yi sanadiyyar kashe sama da fursunoni 50.