Fiye da mutane 200 sun hallaka a Turkiya | Labarai | DW | 14.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fiye da mutane 200 sun hallaka a Turkiya

Ana ci gaba da neman wadanda suke makale bayan fashewar da aka samu a wajen hakar ma'adinai na kasar Turkiya

Masu aikin ceto na kokori zakulo daruruwan ma'aikata da suka makale, lamarin ya faru kusan da garin Soma na yammacin kasar ta Turkiya, kuma an yi imanin akwai ma'aikata kusan a cikin wajen hakar ma'adinan lokacin da aka samu fashewar.

Ma'aikatar kula da makamashi ta kasar ta ce, an fito da kimanin mutane 360 zuwa sanyin safiyar wannan Laraba. Mahukuntan kasar ta Turkiya sun cewa akwai yuwuwar matsalar lartarki ta haifar da fashewar da kuma tashin gobarar da aka samu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman