Fiye da mutane 100 sun hallaka cikin hare hare a Pakistan | Labarai | DW | 11.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fiye da mutane 100 sun hallaka cikin hare hare a Pakistan

Fiye da mutane 100 sun hallaka cikin hare haren bama bamai da aka kai wasu sassan kasar Pakistan

Fiye da mutane 100 sun hallaka cikin hare haren bama bamai da aka kai wasu sassan kasar Pakistan, wadanda ke zama lamari mafi mani da kasar ta fuskanta cikin tashe tashen hankulan da su ka ritsa da ita.

Kuma hare haren sun hada da mutuwan akalla mutane 81, yayin da wasu fiye da 120 su ka samu raunika, lokacin da aka tayar da bam a wajen ibadan 'yan Shiya da ke garin Quetta na yankin kudu-maso yammacin kasar. Sannan wani harin kan ayarin motocin jami'an tsaro a garin ya yi sanadiyar mutuwan mutane 11.

Har ila yau, wasu mutanen 22 sun hallaka wasu fiye da 80 su ka samu raunuka cikin hari na uku, a yankin Swat.

Kasar ta Pakistan mai mutane kimanin milyan 180, ta na kara fuskantan tashe tashen hankula daga kungiyoyi masu zazzafan kishin addinin Islama.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman