Firaministan Libiya ya yi barazanar ajiye aiki | Labarai | DW | 12.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Libiya ya yi barazanar ajiye aiki

Akwai rudani da rashin tabbas kan makomar gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan kasashen ketere bayan firaminista ya yi barazanar ajiye aiki

Firaministan gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan kasashen duniya Abdullah al-Thani ya yi barazanar ajiye aiki, lokacin da yake jawabi a tashar talabijin ta kasar. Ya ce idan tafiyarsa zai kawo karshen matsalolin da kasar take fama a shirye yake domin ya ajiye mukamun. Sai dai kawo yanzu firaministan ya ci gaba da rike mukamun.

Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka tana cikin radanin siyasa da tattalin arziki tun shekara ta 2011, bayan boren da ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40, inda yanzu haka ake da gwamnatoci biyu masu adawa da juna. Majalisar Dinkin Duniya tana shiga tsakanin bangarorin dmoj samar da mafita.