1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

FIFA ta dakatar da Martinez daga buga wasanni

September 28, 2024

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da fitattacen mai tsaron ragar Ajantina Emiliano Martinez daga shiga gasar wasanni guda biyu a nan gaba sakamakon halin rashin da'ar da ya nuna.

https://p.dw.com/p/4lBvf
Mai tsaron ragar Ajantina Emiliano Martinez
Mai tsaron ragar Ajantina Emiliano MartinezHoto: Ulrik Pedersen/Defodi Images/picture alliance

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ajantina (AFA) ita ce ta fitar da sanarwar ta FIFA kan 'dan wasan mai shekaru 32 da ya aikata makamancin laifin da ake tuhumarsa da shi a lokuta daban-daban. Laifukan sun hada da sanya kofin da Ajantinan ta lashe a matse matsi bayan tawagarsa ta doke Chile a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya da kuma jifar da ya yi wa wani 'dan jarida dauke da na'urar daukar hoto da safar hannunsa.

Karin bayani: Ajantina: Nasarar Alberto Fernandez 

Hukuncin FIFA na nufin cewa Martinez ba zai buga wasannin da Ajantina za ta fafata da Venezuela a ranar 10 ga watan Oktoba da kuma Bolivia a ranar 15 ba.