1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FIFA ta dage hukunci kan dakatar da Israila

Abdullahi Tanko Bala
October 3, 2024

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce za ta kaddamar da bincike kan bukatar Falasdinawa na dakatar da Israila daga wasanni.

https://p.dw.com/p/4lNhq
Jibril Rajoub na ahukumar kwallon kafa ta Falasdinawa
Hoto: Sakchai Lalit/AP Photo/picture alliance

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta sanar ta ce ba ta cimma matsaya ba kan hukunci game da bukatar Falasdinawa na dakatar da Israila daga wasanni.

A cikin wata sanarwa FIFA ta ce za ta sa kwamitin ladabtarwa wanda zai yi bincike kan zargin wariya da hukumar kwallon kafa ta Falasdinawa ta gabata tare da ba da shawara ga kwamitin koli.

Shugaban hukumar ta FIFA Gianni Infantino ya ce kwamitin kolin na duba dukkan wani korafi tare da nazari sosai, suna kuma bi sau da kafa shawarwarin kwararru masu zaman kansu.