1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FBI ta gano sirrin gwamnati a gidan Trump

Abdul-raheem Hassan
August 13, 2022

Jami'an leken asiri na gwamnatin Amirka wato FBI, sun bankado wani 'babban sirri' da wasu muhimman takardu kan tsaron kasa a gidan tsohon Shugaban kasar Donald Trump a jihar Florida.

https://p.dw.com/p/4FUMt
Amirka, Trump
Hoto: Metin Aktas/AA/picture alliance

Hukumar FBI ta samu wasu bayanan sirri guda 11 a wani samame da ta kaddamar bisa umarnin kotu a gidan Trump, cikin takardun sirri da hukumar ta bankado har da mahimman bayanan sirrin kasar wadanda idan aka fallasa su a bainar jama'a, za su haifar da mumunar illa ga makomar Amirka.

Wata kotun tarayya ce ta ba wa jami'an FBI damar gduanar da bincike a gidan Donald Trump, kan zargin samun bayanan keta dokokin kasa guda uku, ciki har da adana bayanai da yadasu ko batar da wasu mihimman bayanai da suka shafi tsaron kasa.