Fatali da taimakon G7 | Labarai | DW | 27.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fatali da taimakon G7

Hukumomi a kasar Brazil sun yi fatali da tallafin kudi na dalar Amirka miliyan 20 da taron kungiyar G7 ya yi alkawalin bayar wa ga kasar don tunkarar gobarar dajin Amazon da yanzu haka ke cigaba da ruruwa.

Da yake mayar da maratani ga matakin tallafin jim kadan bayan kammala taronsu a birinin Biarritz na kasar Faransa, darakatan fadar shugaban Brazil ya cewa tayin tallafin  akai kasuwa, inda ya caccaki shugaba Emmaneul Macron na Faransa da ya bayyana sanarwar agajin kudin, yana mai cewa da ya mayar da hankalinsa ga kasashen da Faransa ta yiwa mulkin mallaka maimakon Brazil, kana kuma ya ce ta kaka shugaban da ya kasa daukar matakin hana gobara a majami'ar Notre Dame, zai ba da wani misali ga kasar ta Brazil.