Fargabar komawa gidan jiya a Mozambik
October 25, 2013Jaridun a wannan makon sun fi mayar da hankali ne a kan rikicin da ya kunno kai a kasar Mozambik. A labarinta da ta rawaito madugan yaki na cewa "shekaru 21 na zaman lafiya ya isa hakan" jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi.
Kasar Mozambik na daya daga cikin kasashen Afirka da ake sa ran za su samu bunkasa. Godiya ta tabbata da arzikin gas, masu zuba na layin samun shiga wannan matalauciyar kasa. Amma tana barazanar fadawa rikici shigen wanda ta yi fama da shi a baya, biyo bayan sanarwar da kungiyar adawa ta Renamo ta bayar cewa ta yi bankwana da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 1992, kana ta koma fagen yaki. Renamo wadda bayan kawo karshen yakin basasan kasar ta rikide zuwa jam'iyyar siyasa ba ta taba zama barazana ga Frelimo mai jan ragamar mulki ba. Shekaru uku da suka wuce karin farashin kaya abinci ya janyo wata zanga-zanga a babban birnin kasar Maputo, wadda aka murkusheta da karfin tuwo. Kuma kusan shekara guda da ta wuce jagoran Renamo Dhlakama ya kafa sabuwar hedkwata a kan tsunukan Gorongosa dake tsakiyar kasa. Sannan a watan Maris na wannan shekara an fara kai hari da makamai a kan matafiya tsakanin Maputo da birnin Beira mai tashar jiragen ruwa. An zargi Renamo da kai hare-haren sannan tun a watan Afrilu an yi fadace-fadace tsakanin magoya bayan Renamo da kuma 'yan sanda.
Gwagwarmayar neman iko ta rikide zuwa yaki
Zaman lafiyar shekaru 20 da aka samu a Mozambik ya ruguje inji jaridar Berliner Zeitung tana mai cewa gwagwarmayar neman madafun iko tsakanin tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta Renamo da jam'iyyar Frelimo dake jan ragamar mulki ta rikide zuwa fada gadan-gadan. Bayan wani farmaki da dakarun gwamnati suka kai kan hedkwatar Renamo dake yankin Gorongosa, tsohuwar kungiyar 'yan tawayen ta ba da sanarwar janyewa daga yarjejeniyar zaman lafiya da suka kulla da jam'iyar Frelimo. Bayan kawo karshen yakin basasan a 1992, al'ummar kasar ta Mozambik su kimanin miliyan 25 sun samu bunkasar tattalin arziki bayan da Frelimo wadda a da ke zaman mai bin tsarin gurguzu ta koma wata jam'iyya mai bin tsarin jari hujja.
Kariya ga 'yan gudun hijira na hakika
Bai kamata tekun Bahar Rum ya zama wani babban kabari ba, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai mayar da hankali a kan dubban bakin haure dake bi ta wannan hanya mai hadari a kokarin shigowa nahiyar Turai. Bayan sukar manufofin tarayyar Turai da suke zama karfen kafa ga bakin masu neman mafakar siyasa da ingantuwar rayuwa, jaridar kira ta yi tana mai cewa.
"Kamata a samar wa mutanen da ke neman kariya daga gamaiyar kasa da kasa, kyakkyawawan hanyoyin shigowa Turai. Kamata ya yi kuma hukumar tarayyar Turai ta hada kai da babbar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya domin samun sabbin matsugunai ga wadannan mutane. Ta ce wajibi ne kungiyar EU da kasashen da kawo yanzu ba su da kyakkyawan tsarin ga 'yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa, su shiga cikin shirin samar da sabbin matsugunai. Dole ne a tabbatar cewa 'yan gudun hijira na hakika dake bukatar kariya kamar yara da tsoffi da kuma marasa lafiya a ba su damar shigowa Turai ta kyakkyawawan hanyoyi."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman